Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya isa Mashhad ne bayan ya halarci birnin Najaf Ashraf, inda ya kasance cikin ayarin da ya raka gangar jikin Imam Shahidi daga Najaf zuwa Mashhad domin a binne ta a Haramin Imam Ali bn Musa al-Ridha (AS).
Rahotanni sun ce jagoran Harkar Musulunci ya yi tafiyar ne tare da ayarin jana'izar tun daga Najaf Ashraf, kafin ya isa Mashhad, inda ya shiga cikin dimbin malamai, jami'ai, da al'ummomi daga sassa daban-daban na duniya da suka hallara domin yin bankwana da girmamawa ga Shahidin jagoran al'ummar Musulmi.
Ana sa ran za a gudanar da jana'iza da kuma binne gangar jikin Imam Shahidi, Ayatullahil Uzma Imam Sayyid Ali Khamene'i (QS), a Haramin Imam Ridha (AS), tare da halartar taron jama'a masu tarin yawa, malamai, masana, da wakilai daga ƙasashe daban-daban na duniya.






Ra'ayinka